(ABNA24.com) Hukumar kula da bakin haure ta MDD, ta fitar da wani rahoto dake cewa mutane kimanin 23,000 ne sukayi hijira zuwa Nijar, a cikin watan Afrilu da ya gabata domin gujewa tashe tashen hankulan dake faruwa a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Wannan a cewar hukumar ya sanya adadin ‘yan Najeriyar da sukayi hijira zuwa kasar ta Nijar, tun daga watan Afrilun bara, ya haura sama da 60,000.
Rahoton ya ce mutanen dake neman kare rayuwarsu, sun keta iyakokin kasar ta Nijar duk da kasancewarsu a rufe sakamakon annobar cutar Korona.
Hukumar ta UNHCR, ta ce galibin mutanen sun kasance ne mata da yara da suka fito daga jihohin Sokoto, Zamfara da kuma Katsina, sakamakon hare hare ‘yan bindiga da kuma hare haren martani da jiragen saman sojojin Najeriyar ke kaiwa musamman a watan Afrilun da ya gabata.
HCR, ta ce ta damu matuka game da halin da mutanen ke ciki a jihar Maradi ta Nijar, inda suke da matukar bukatar ababen yau da kulun da kuma matsugunni.
/129
13 Mayu 2020 - 06:20
Lambar labari: 1036344
Hukumar kula da bakin haure ta MDD, ta fitar da wani rahoto dake cewa mutane kimanin 23,000 ne sukayi hijira zuwa Nijar, a cikin watan Afrilu da ya gabata domin gujewa tashe tashen hankulan dake faruwa a yankin arewa maso yammacin Najeriya.